Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban malamin addini Sheikh Muntaka Bashir Mbaki wanda aka haifa a cikin shekara ta 1934 a garin Tuba na Senegal ya zama jagoran mabiya darikar Murdiyyah a fadin kasar da kewaye.
Malamin ya shara wajen ilimin kur’ani mai tsarki tare da koyar da shi da ma sauran ilmomin addini, ya kuma yi karatu ne a wajen mahaifinsa tun lokacin kuruciya.
An zabe shi domin maye gurbin tsohon jagoran wannan darika ta sufaye wanda Allah ya yi masa rasuwa a makon da ya gabata.
Sheikh Bashir Mbaki yam aye gurbin marigayi sheikh Mukhtar Mbaki ne bisa cancanta ta fuskar ilimi da kuma talu’u gami da sauran siffofin da ake dubawa kafin zabar mutum a kan wannan matsayi.